Muna Alfahari da irin Ayyukan Alheri da kake yi – Gwamna Nasir ya yabawa Enabo

Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, ya yabawa shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Faruk Musa Yaro (Enabo), bisa shirya gagarumar aikin tallafawa al’umma mafi girma a tarihin jihar.
Shirin wanda ke karkashin gidauniyar Alhaji Faruk Enabo Foundation ya amfani sama da mutane 10,000 dake unguwar Marafa ta karamar hukumar Birnin Kebbi da motoci 50, babura 100, famfunan ruwa 50, buhunan hatsi iri-iri 5,000, da rigar wasanni, da tallafin kudi da ya kai naira miliyan 250.
Gwamna Idris ya yabawa Enabo bisa tunawa da magoya bayan jam’iyyar APC, ya kuma bukaci ‘yan siyasa da masu rike da mukamai da su yi koyi da shi.
Ya nanata cewa dimokuradiyya ita ce karfafawa al’umma, ya kuma kara jaddada aniyar gwamnatinsa na bullo da shirye-shirye masu yawa na tallafawa musamman mata, matasa, da manoma ta hanyar takin zamani da kayan noma kyauta.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kebbi da su ci gaba da marawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC goyon baya, inda ya ce Tinubu ya kawo ayyuka da dama a jihar kuma ya cancanci a sake zaben shi a karo na biyu.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kebbi kuma Ministan Kasafin Kudi da Tsare tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yaba wa Enabo tare da yin kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su rika maimaita irin wadannan abubuwan a garuruwan su.
