Mun samu barazanar kai hari a Majalisar Dokoki ta Kasa – ‘Yan Majalisa

0
1000211347
Spread the love

Shugaban Kwamitin Tsaron Cikin Gida na Majalisar Wakilai, Garba Muhammad, ya ce Majalisar Dokokin ta samu barazanar kai hari daga ‘yan ta’adda.

Garba ya bayyana hakan ne a wani zaman sauraron jama’a kan kudirin da ke neman kafa Hukumar Tsaron Majalisar Dokoki, wacce ke neman inganta harkokin tsaro, kare ‘yan majalisa, ma’aikata da kuma masu zuwa majalisar dokokin kasar.

A cewarsa, cibiyar na fuskantar kalubalen tsaro, ciki har da satar motoci da babura, lalata kayayyaki, katunan shaida na bogi, da kuma kutse daga bakin da ba su yi rijista ba.

Rahoton DAILY POST ta bayyana cewa an yi wani lamari makamancin haka a ranar 4 ga Mayu, 2021, lokacin da aka yi gargadin tsaro ga ‘yan majalisa game da wani shirin kai hari kan ginin Majalisar Dokoki ta Kasa da sauran wuraren gwamnati a Abuja.

Bayan gargadin, Majalisar Dokoki ta Kasa ta takaita kasancewar ‘yan majalisa a harabar majalisar don tsaro, kuma kwararrun tsaro sun yi kira da a kara karfafa tsaro ga kayayyakin more rayuwa da kadarorin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *