Mummunan yanayi ya kashe mutum uku a sansanin gudun hijira na jihar Neja

Mutum uku sun mutu a sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankunan Shiroro da Munya a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
Hussaini Alhassan ɗaya ne daga cikin masu kula da sansanin Gwada, kuma ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa mutanen sun mutu ne saboda ƙarancin kayayyakin kula da lafiya da kuma abinci.
Bayanan sun fito ne a lokacin da ƙungiyar North South Power Foundation (NSPF) ta kai ziyara domin raba tallafin kayan abinci da suka kai darajar naira miliyan 30 a ranar Asabar.
Alhassan ya ce akasarin ‘yan gudun hijirar sun tsere ne daga garuruwan Kaore da Bassa saboda hare-haren ‘yanfashin dajiShi ma wani jami’i a sansanin Kuta, Yusuf Kuta, ya tabbatar da mutuwar wata dattijuwa a sansanin, abin da ya sa suka zama uku.
