‘Ba zan huta ba, sai mun ceto mutanenmu da aka sace’

0
1000473780
Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Gwamnan ya ce yana bibiyar ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi game da batun, kuma ba zai gajiya ba har sai an yi nasarar ceto dukkan mutanen da aka sace.

A ranar Lahadi wasu mahara suka shiga ƙauyen Kurmin Wali inda rahotanni ke cewa sun yi garkuwa da mutane fiye da 170 tare da jefa al’ummar yankin cikin ruɗani.

Da farko ƴansanda da jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun musanta faruwar lamarin amma daga baya suka fitar da sanarwar da ke tabbatar da shi, duk da cewa kawo yanzu babu haƙiƙanin bayani kan ko mutane nawa ne aka sace a ƙauyen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *