Mataimakiyar Gwamnar Adamawa ta Jaddada goyon bayan Gwamnati ga shata Iyakokin Najeriya Da Kamaru

0
1000305969
Spread the love

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Adamawa Farfesa Kaletapwa Farauta ta jaddada goyon bayan gwamnati ga warware matsalar tsara shata iyakoki tsakanin Najeriya da KamaruFarauta ta ba da tabbacin hakane a ofishinta, lokacin da Darakta Janar na Hukumar Kula da Iyakoki ta Kasa (NBC) Adamu Adaji ya ziyarci ofishinta ranar Talata a Yola.

Ta ce tuni an wayar da kan mazauna yankunan da abin ya shafa da kuma bukatar yin aiki tare da jami’ai daga kasashen biyu.

Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Kula da Iyakoki ta Kasa, Adamu Adaji ya ce tawagarsa ta kasance a jihar don sanar da gwamnati da mutanen jihar cewa hukumar ta kammala tsara taswirar iyakoki kuma za ta fara shata iyakoki a shekara mai zuwa.

Idan za’a a tuna dai a baya Kwamitocin Iyakokin Jihohi na jihohin da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru sun nada Mataimakiyar Gwamnan na Adamawa, a matsayin Shugaban kwamitin.Jihohin da ke kan gaba sun hada da Adamawa, Borno, Taraba, Benue Cross River da Akwa Ibom.

Farauta, ta bayyana muhimmancin dandalin tattaunawar wajen inganta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Kamaru, inda ta kara da cewa hadin gwiwar zai yi aiki tare da muradun tsaron kasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *