Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima da Zulum Sun Ziyarci Wadanda Bam ya ritsa dasu a Masallacin Maiduguri

0
1000403635
Spread the love

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Juma’a, sun ziyarci wadanda harin bam din ya rutsa da su a ranar Laraba a wani Masallaci da ke Maiduguri, wadanda a halin yanzu ake kula da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Harin, wanda ake kyautata zaton ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka kai, ya haifar da asarar rayuka da dama da kuma raunuka.

A asibitin, yayin da yake magana da manema labarai, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, wanda ke tare da Gwamna Zulum, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa kuma ya sake nanata kudirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kawo karshen barazanar ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *