Masu zanga-zanga na ci gaba da mamaye majalisan dokokin Najeriya

0
1000523817
Spread the love

Haɗin gwiwar ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin matasa da kuma ‘yan ƙasa masu rajin kishin demokradiyya sun taru a harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa don neman a amince da gyaran dokar zaɓe nan take, musamman tanadin aika sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura kafin babban zaɓen 2027.

Masu zanga-zangar sun ce gyaran ya zama dole don inganta gaskiya da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin zaɓen Najeriya.

Daga cikin masu zanga zangar akwai mambobin jam’iyyar African Democratic Congress ADC a wurin.

Gangamin dai ya kasance cikin kwanciyar hankali zuwa yanzu, inda jami’an tsaro da suka haɗa da haɗin gwiwar ƴan sanda, Sojoji da kuma jami’an tsaron farar hula na Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *