Mali ta maka Algeria gaban kotun duniya ta ICJ

Gwamnatin mulkin soji a Mali ta shigar da ƙarar makociyarta Algeria a gaban Kotun duniya ta ICJ, inda ta ke zarginta da cutar da ita da gangan bayan da ta kakkabo da wani jirgi marar matuƙi mallakinta da ta tura wani yanki mai ɗauke da mayaƙa ƴan tawaye, a cikin watan Maris da ta gabata.
Ƙarar da gwamnatin Mali ta shigar a Kotun duniya ta ICJ na da alaƙa da kakkabe jirgi marar matuƙi mallakin Turkiyya da Algeria ta yi, wanda ya faru a daren 31 ga watan Maris da ya gabata kusa da kan iyakar Tinzaouaten, a yankin Kidal.
Sanarwar da ma’aiakatar kula da kan iyakar Mali ta fitar na cewa ƙasar na zargin Algeria da aikata hakan ne dan hana sojojinta samun damar afkawa ƴan tawaye masu riƙe da makamai a yankin.
Sanarwar ta kuma ce ya zuwa yanzu Algeria ta kasa gabatar da shaidar da ke nuna cewa jirgin ya shiga ƙasarta ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda ya sabawa dokokin ƙasa da ƙasa, kuma kawo yanzu bata ce uffan a game da faruwar lamarin ba.
Kwanaki bayan faruwar lamarin ne gwamnatin soji ta Mali da Burkina faso da kuma Nijar suka buƙaci jakadodinsu da ke Algeria su koma gida don nuna adawarsu da faruwar lamarin.
Daga bisani Algeria ta rufe sararin samaniyarta a wani mataki na hana shiga da fitar jiragen sama zuwa Mali, kazalika ta bi sahun takwarorinta na kiran jakadodinta su koma gida.
