Majalisar Musulmin Adamawa ta ziyarci Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, inda ta jaddada goyon bayansu

Majalisar musulmin jihar Adamawa ta kai ziyarar ban girma ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnati dake Yola.
Tawagar wadda shugaban Majalisan Mallam Gambo Jika ya jagoranta, ta yabawa gwamnan bisa manufofin sa na ci gaban al’umma da ci gaban jihar.

A yayin ziyarar majalisar ta kada kuri’ar amincewa da Gwamna Fintiri, inda ta bayyana gwamnatinsa a matsayin mai hada kai da kuma biyan bukatun al’umma.
Mallam Gambo Jika, a nasa jawabin, ya tabbatarwa Gwamnan goyon baya da addu’o’in samun nasarar gwamnatin sa.

Gwamna Fintiri, a lokacin da yake mayar da martani, ya yabawa majalisar musulmi bisa karramawar da suka yi masa, ya kuma yi alkawarin ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a jihar Adamawa.
