Majalisar matasan Plateau ta yi watsi da ikirarin cin zarafin da kungiyar Fulani ke yi

Kungiyar matasan Plateau, PYC, ta yi watsi da furucin da wata kungiyar Fulani mai suna Coalition of Fulani Registered Organisation, COFRO, ta yi na cin zarafi da kuma kabilanci da hukumomin tsaro ke yi musu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar Fulani ta yi zargin cewa, a duk lokacin da rikici ya barke a jihar Filato, a bisa rashin adalci ana daukan makiyaya a matsayin ’yan ta’adda, inda suka bayyana cewa, Fulani su ne ma wadanda akafi kashewa a mafi yawan rikice-rikicen.
Shugaban kungiyar na karamar hukumar Bokkos Sale Yusuf Adamu, ya ce kungiyar ta yi watsi da cewa Fulani ‘yan ta’adda ne kaamn yadda ake alakantawa a tashe tashen hankulan da ke faruwa a jihar, inda suka tabbatar da cewa su ne wadanda abin ya shafa.
Sai dai a martanin da kungiyar ta Fulani ta yi, kungiyar Bokkos ta PYC ta bayyana zargin a matsayin mara tushe bare makama.
