Majalisar jihar Rivers ta sake ƙaddamar da shirin tsige Fubara

0
1000440195
Spread the love

Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake ɗaukar zafi bayan majalisar dokokin jihar ta sake ƙaddamar da shirin tsige gwamna Siminilaya Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu.

An bijiro da maganar tsige gwamna ne a zaman majalisar na ranar Alhamis, 8 ga watan Janairun 2026.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya karanta takardar neman majalisar ta ƙaddaamar da shirin tsige gwamnan, bisa zargin shi da aikata manyan laifuka da ya ce sun saɓa da doka.

Ya ce sun yi la’akari da sashe na 188 ne na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tattarawa da tantace laifukan da suke ganin gwamnan ya yi, waɗanda kuma suke ganin sun saɓa da doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *