Majalisan Musulman Taraba sun haramta bukukuwan Ƙauyawa lokacin aure

0
1000090499
Spread the love

Majalisar Musulunci a Jihar Taraba dake Najeriya ta haramta wasu bukukuwan auren da matasa ke yi wanda suka ce ya saɓawa addinin Islama, saboda yadda ake cuɗuwa tsakanin samari da ƴam mata.

Daga cikin bukukuwan da aka hana lokacin aure harda wanda ake kira ’Kauyawa Day’ da Ajo wanda ake ganin maza da mata na sanya yagaggun tufafi da kuma tikar rawa har zuwa tsakiyar dare.

Taron limaman Masallatan jihar ne ya amince da matakin a Jalingo, lokacin da suka gudanar da taro na musamman a ƙarƙashin Majalisar Musulunci ta jihar.

Limaman juma’an sun yi amfani da huɗubar juma’ar da ta gabata wajen janyo hankalin jama’a a kan ɗaukar matakin gyara saboda illar da waɗannan halaye ke yiwa addinin Islama.

Malaman sun ce daga yanzu duk wanda ya saɓawa wannan umarni, zai gamu da fushin majalisar wajen ƙin ɗaura auren gidansa, ko zanen suna ko kuma jana’izar da aka samu a tsakanin iyalan gidan.

Majalisar ta janyo hankalin jama’a da su mutunta wannan umarnin wanda aka bada shi domin tsaftace al’umma da kuma dawo da su a kan tafarkin tsira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *