Majalisan dattawa tayi watsi da maganan dawowar Natasha bakin aiki

0
1000146429
Spread the love

Majalisar dattawa ta Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, inda ta ce har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba.

Natasha ta rubuta wasiƙa ne a ranar 8 ga Agustan bana, inda a ciki ta sanar da majalisar shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, inda ta ce wa’adin wata shida da aka dakatar da ita ya cika.

Ta ce kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yuln da ya gabata cewa dakatarwar da aka mata ba daidai ba ne, sannan ta umarci majalisar ta mayar da ita bakin aiki.

Amma a wata wasiƙar martani da majalisar ta rubuta a ranar 4 ga Satumba, wadda muƙaddashin akawun majalisar, Yahaya Danzaria ya sanya wa hannu, ya ce ba za ta koma bakin aiki ba har sai an kammala shari’ar lamarin a kotu.

Ya ce, “wannan maganar tana gaban kotu, kuma majalisar ba za ta yi komai a game da batun komawarki bakin aiki ba har sai kotu a kammala shari’ar baki ɗaya. Don haka a yanzu babu abin da ofishinmu zai iya yi a game da wannan batu.”

A ranar 6 ga watan Maris ne dai majalisar dattawa ta dakatar da sanatana bayan ta yi musayar yawu da shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *