Likitocin Asibitin koyarwa na Yola sun raba wasu tagwaye biyu dake haɗe

0
IMG-20260310-WA0013
Spread the love

Tawagar kwararrun likitoci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Jihar Adamawa, ta yi nasarar raba tagwaye maza dake haɗe da juna na watanni huɗu a cikin wani aikin tiyata mai sauƙi.

Tiyatar, wacce ƙwararren likitan tiyatar yara Farfesa Abubakar Auwal ya jagoranta, ta ɗauki kimanin awanni uku kuma ta ƙunshi raba jariran dake haɗe.

A cewar tawagar likitocin, wannan aikin ya zama na shida da aka yi nasarar raba tagwayen dake hade a asibitin, wanda ya nuna ƙwarewar da cibiyar ke da ita a cikin ayyukan tiyatar yara masu irin wannan matsalan.

An yi wannan tiyatar kyauta, tare da tallafi daga Asusun tallafawa Ilimi na (TETFund), wanda ya zuba jari a binciken lafiya da kayan aiki a asibitin.

Masu kula da asibitin sun yaba wa likitocin da suka jagoranci tiyatar kuma sun lura cewa asibitin koyarwan ya zama babban cibiya don tiyatar yara ta musamman a Najeriya, wanda ke jawo hankalin marasa lafiya daga ko’ina cikin ƙasar.

Mahaifin tagwayen, wanda ya fito daga Jihar Taraba, ya nuna godiyarsa ga asibitin don ceton rayukan ‘ya’yansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *