Lakurawa sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar Kebbi

0
1000262512
Spread the love

Ƴanbindiga da ake zargin Lakurawa ne sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar jihar Kebbi Samaila Bagudo.

Rundunar ƴansandan jihar Kebbi sun tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ta ce ƴanbindigar sun auka gidan ɗanmajalisar ne da misalin bayan sallar Isha a hanyarsa ta komawa gida.

Kakakin rundunar CSP Nafiu Abubakar ya ce an tura jami’an tsaro yankin domin su ceto shi.

Rundunar ta sake nanata za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuwa da dukiyar al’ummar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *