Kwatsam ta kama makamai da ƙwayoyin N10bn a Legas

0
20250430_010007
Spread the love

Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya.

Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista.

“A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya kan waɗannan kaya ya haura Naira biliyan 10,” in ji Shugaban Hukumar.

Kayan da aka kama sun haɗa da:

– Bindigogi biyu na pump-action, bindiga ɗaya nau’in Smith & Wesson da harsasai fiye da 80

– Kwalaye 202 na kayan maye (Colorado Loud), nauyinsu ya kai kilo 101

– Kwantainoni 7 na magungunan da suka daina da haramtattu

– Kwantainoni 3 na abinci da ya lalace.

– Kwantainoni 3 na haramtattun tufafi

– Kwantainoni 2 ɗauke da magungunan codeine

– Kwantaina ɗaya da ke ɗauke da kwalaye 305 na man goge baki na ƙarya da aka ɓoye da ɗinki da kayan ado

Adeniyi ya ce an gudanar da binciken tare da haɗin gwiwar Hukumar NDLEA da sauran hukumomin gwamnati.

Ya jaddada cewa har yanzu an dakatar da amfani da tashoshin wajen fitar da magunguna.

An kama mutane biyar, inda uku daga cikinsu aka gurfanar da su kuma suna tsare a gidan yari na Ikoyi har sai an fara shari’ar su.

Hukumar Kwastam ta ce tana aiki da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa don gano tushen waɗannan kaya da hana Najeriya zama wurin zubar da haramtattun kaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *