Kungiyar Fulani ta zargi matasan Agatu da kai hare-hare ba gaira ba dalili, da kisa, da satar shanu cikin makonni uku

0
1000211378
Spread the love

Wata kungiyar al’adu ta Fulani mai suna Voice of Fulbe mai neman zaman lafiya da ci gaba, ta zargi wasu matasa a yankin Agatu ta Yamma a karamar hukumar Agatu, a jihar Benue da ci gaba da kai munanan hare-hare da kashe-kashe da kuma satar shanu ga Fulanin da ke zaune a jihar Kogi.

Sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Hamman Gizo da Sakatare Ardo Ibrahim Yallo, sun bayyana hare-haren a matsayin wanda bai dace ba, kuma sun dora laifin kashe wasu da ake zargin matasa da aikata laifukan da suka yi sanadiyar mutuwar al’umma tare da asarar daruruwan shanu.

Kungiyar ta ce tana wannan kiran ne domin sanar da ‘yan Najeriya, da kasashen duniya, da shugaban Najeriya, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, babban hafsan tsaron kasa, babban hafsan soji, daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami’an tsaro game da irin zaluncin da matasan Agatu suke yi musu.

Kungiyar ta yi zargin cewa rikicin ya kara kamari ne musamman bayan da makiyayan suka bar garin Agatu zuwa jihar Kogi inda suka zauna a can ba tare da wani nufi ko wani tashin hankali ga mutanen Agatu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *