Kungiyar agaji ta Red Cross ta sake duba martanin da aka mayar kan ambaliyar ruwa a Adamawa, ta yaba wa sojoji da ‘yan sanda

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta bayyana cewa ayyukan hadin gwiwa na sojoji da ‘yan sanda ne suka ceto mutanen da suka makale a ambaliyar ruwa ta watan Yuli a karamar hukumar Yola ta Kudu, dake jahar jihar Adamawa.

Da yake magana da manema labarai a ranar a Yola, yayin taron sa ido kan ambaliyar ruwa bayan taron masu ruwa da tsaki da ke da hannu wajen wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa, Jami’in Kula da Bala’oi na jihar Adamawa, Bello Mohammed, ya ce mutanen da dama sun makale a cikin ambaliyar ruwa, amma kuma cikin gaggawar shiga taimako na sojoji da ‘yan sanda an ceci rayuwarsu.

Ya kara da cewa taron yana da nufin yin nazari kan ayyukan hukumomin a lokacin bala’in ambaliyar ruwa na 2025 da kuma gano wuraren da ya kamata a inganta.
Shi ma da yake magana da manema labarai, mai kula da sashen DMO a hedikwatar Red Cross ta Najeriya, Mista Timothy Yohanna, ya nuna cewa kafin ambaliyar ruwan tayi ta’adi a kananan hukumomi bakwai, kamar yadda NIMET ta annabta, kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta dauki ma’aikatan ta da suka kai 210 na wayar da kan jama’a a kananan hukumomi inda ake hasashen ambaliyar ruwa.

Yohanna ya lura cewa taron sa ido kan ambaliyar ruwa bayan an yi shi ne don tabbatar da darussan da aka koya da kuma ra’ayoyin da aka tattara yayin kula da ambaliyar ruwa a Jihar Adamawa.
A cewarsa, taron zai taimaka wa kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da sauran hukumomin da ke da hannu a kula da bala’in ambaliyar ruwa don shiryawa sosai don fuskantar ambaliyar ruwa da ake sa ran za ta faru a shekarar 2026.
Mai kula da hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Mista Namarju Philip, ya ce ambaliyar ruwa ba wai kawai ta faru ne sakamakon ruwan sama mai karfi ba, har ma da karuwar ruwa daga koguna.
