Kotun ƙolin Venezuela ta umarci mataimakiyar shugaban ƙasar ta karɓi mulki

0
1000429036
Spread the love

Kotun Kolin Venezuela ta bayar da umarni ga mataimakiyar shugaban ƙasar, Delcy Rodriguez ta kama aikin shugaban ƙasar a matsayin mai riko, saboda abin da ta kira rashin kasancewar Mista Maduro – na tilas.

A ranar Asabar ne Amurka ta kama shugaban ƙasar da mai ɗakinsa tare tafiya da su ƙasarta kan zargin hada-hadar miyagun ƙwayoyi da makamai- zargin da ya sha musantawa.

Idan aka same shi da laifi za a iya yi masa ɗaurin rai da rai.

Tun da farko Ms Rodriguez, ta yi wani jawabi kakkausa a ranar Asabar, inda ta zargi Amurka da sace Maduro, tana mai cewa Venezuela ba za ta taɓa zama wani yanki na mulkin Amurka ba.

Ta bayyana hakan ne duk kuwa da kalaman Trump cewa ta bayyana aniyarta ta yin aiki tare da gwamnatin Amurka a wata tattaunawa da jami’ansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *