Kotu za ta yanke hukunci kan makomar takarar Maurice Kamto a babban zaɓen Kamaru.

0
1000050706
Spread the love

A yau Talata ne Kotun Tsarin mulki a Kamaru za ta yanke hukunci kan ƙarar da jagoran ƴan hamayyar ƙasar, Maurice Kamto ya shigar na ƙalubalantar matakin soke damarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a watan Oktoba.

Shi ne mutumin da ya zo na biyu a zaɓen 2018 da aka gudanar kuma ana ganinsa a matsayin babban abokin karawar shugaba Paul Biya mai shekara 92 wanda ya shafe shekaru arba’in yana mulki.

Hukumar zaɓen Kamaru ta ce jam’iyyar Mista Kamto ta MANIDEM ta gabatar da ƴan takara biyu da za su yi mata takara ba bisa ƙa’ida ba.

Lokacin da jagororin jam’iyyar suka yi ƙoƙarin gudanar da taron manema labarai domin musanta hakan, sai jami’an tsaro suka hana su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *