Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar Kanu ta canza masa gidan yarin Sokoto

Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ƙi amincewa da buƙatar da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, ya gabatar na neman a canza masa gidan yarin da yake a Sokoto zuwa wani kurkuku da ke cikin Abuja ko Jihar Nasarawa.
Kanu, ta hannun hukumar da ke tallafawa raunan da shari’arsu, ya shigar da ƙara ta gaggawa yana neman umarnin da zai saka gwamnatin tarayya ko hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta hanzarta mayar da shi daga Sokoto zuwa Kuje a Abuja ko Keffi a Nasarawa domin samun damar bin diddigin ɗaukaka ƙarar da yake shirin yi.
Sai dai a ranar Litinin, mai shari’a Omotosho ya ƙi amincewa da bukatar, yana mai cewa ba za a iya bayar da irin wannan umarni ba tare da jin ta bakin gwamnatin tarayya ba.
Kotun dai ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga Janairu, 2026.
A ranar 20 ga Nuwamba, kotu ta same shi da laifi kan dukkan tuhumar ta’addanci guda bakwai da Gwamnatin tarayya ta shigar, tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
