Kotu ta soke belin Malami, ta kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a Kuje
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke belin da aka baiwa Abubakar Malami, Kotun ta yanke hukuncin cewa tunda aka fara shari’ar a baya, an soke dukkan shari’o’in da suka gabata ciki har da belin da Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar – don haka ana bukatar a sake neman belin.
PUNCH ta ruwaito cewa EFCC ta shigar da kara 16 a kan tsohon babban lauyan gomnatin kan zargin halatta kudaden haram da kuma mallakar kadarorin da suka kai sama da Naira biliyan 8.7 ba bisa ka’ida ba.
A zaman sauraron karar, masu gabatar da kara, karkashin jagorancin Jibrin Okutepa, sun sun nemi a duba bukatun wanda ake kara kan tuhume-tuhume 16 da aka yi wa kwaskwarima.
