Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP

A karo na biyu, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana Jam’iyyar PDP gudanar da Babban Taronta na Kasa na 2025 da aka shirya gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo tsakanin 15 zuwa 16 ga Nuwamba.
Kotun ta kuma hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, sa ido, ko amincewa da sakamakon Babban Taron Kasa inda ake sa ran za a zabi shugabannin Jam’iyyar.
A ranar Talata ne Alkali Peter Odo Lifu ya bayar da sabon umarnin yayin da yake yanke hukunci a cikin wata bukata da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya gabatar.
Lamido, wanda yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, ya shigar da kara a gaban kotun yana korafin cewa an hana shi damar sayen fom din takarar Shugaban Jam’iyyar don ba shi damar shiga taron.
Alkalin ya yi hasashen umarnin takaitawa kan PDP bisa dalilin cewa jam’iyyar ta ki, ta yi sakaci da kuma kin bin ka’idoji da dokoki masu dacewa don gudanar da irin wadannan tarurruka.
