Kotu ta kama mutum 10 da laifin cin zarafin matar shugaban Faransa ta intanet

Wata Kotu a Paris ta kama mutum 10 da laifin cin zarafin matar shugaban Faransa Brigitte Macron ta intanet.
Mutanen sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa jita jita inda suke nanata cewa matar shugaban ƙasar ba ita bace ba ɗanuwanta ne Joe Michel da aka yi wa sauyin jinsi.
Haka kuma, sun zargi matar shugaban ƙasar da aikata cin zarafi ta hanyar lalata kan Emmanuel Macron sakamakon cewa kwai bambancin shekaru 24 a tsakaninsu.
Sun wallafa ƙarairayin ne a shafukan intanet inda dubban daruruwan mutane suka karanta.
Kotun ta bayyana cewa ƙarairayin da suka wallafa sun bazu sosai a intanet, inda dubban mutane suka karanta su.
A hukuncinta, kotun ta yanke musu gargadin ɗaurin watanni takwas tare da tilasta musu neman ilimi kan kaucewa cin zarafi ta intanet.
