Kotu ta daure tsohon Prime Ministan Thailand

Kotun Kolin Thailand ta daure tsohon firaiministan kasar Thaksin Shinawatra.
Alkalin kotun da ke Bangkok, ya shaida masa cewa ba abi tsarin shari’a ba wajen tsare shi da aka yi a wani asibiti bayan an same shi da laifin aikata cin hanci.
Daga nan ya bayar da umarnin cewa za a tsare Mr Thaksin a gidan yari tsawon shekara guda.
Tsohon firaiministan na Thailand ya amince da hukuncin inda ya ce zai yi dukkan abin da aka umarce da yi ba tare da wata matsala ba.
A watan da ya gabata ne aka tursasa wa ‘yarsa Shinawatra yin murabus daga mukamin firaiminista.
