Kiraye-kirayen cewa na ajiye takara cin amanar ƴan Najeriya ne – Atiku

Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi gargaɗi kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya ajiye takara a yaƙin neman shugabancin kasa ƙarkashin jam’iyyar haɗaka ta ADC, yana mai cewa hakan cin amanar ‘yan Najeriya ne.
Sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na ganin Atiku ya ajiye takara zai goyi bayan manufofin kama-karya ne kawai tare kuma da tauye hakkin dimokuradiyya a Najeriya.
Sanarwar ta ce a cikin shekaru kusan uku da suka gabata, ‘yan Najeriya sun fuskanci wahalhalu masu tsanani sakamakon manufofin tattalin arziƙi a ƙarkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanarwar ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da ƙoƙarin mayar da siyasar Najeriya ta zama ƙarƙashin jam’iyya ɗaya ta hanyar raunana jam’iyyun adawa.
