Jirgin kasa da ya taso tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya kauce hanya.

0
1000094235
Spread the love

A safiyar ranar Talata ne wani jirgin kasan fasinja da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kauce hanya, inda matafiya da dama suka makale.

Lamarin ya afku ne a babban titi jim kadan bayan jirgin ya taso daga Abuja da misalin karfe 11 na safe, kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.

An gano cewa wurin ya kasance cikin hargitsi, inda jama’a suka yi ta tururuwa domin tsira cikin fargaba da rudani.

Kawo yanzu dai ba a san abin da ya jawo karkacewar jirgin ba, kuma babu wani tabbaci a hukumance na rauni ko asarar rayuka.

A cewar rahoton, an tura jami’an soji zuwa wurin domin taimakawa wajen kwashe fasinjojin da suka makale.

Sai dai har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *