Jam’iyyar APC ta Adamawa ta kaddamar da aikin yin rijista ta hanyar intanet

0
1000321386
Spread the love

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta kaddamar da aikin yin rijistar ta yanar gizo.

A wani taro da aka gudanar domin sanar da kammala shirye-shiryen yin rijistar a ranar Litinin a Yola, jam’iyyar ta umarci shugabanninta da su tabbatar da cewa sabbin mambobi 200,000 sun shiga cikin wannan shiri a cikin watan farko na yin rijistar.

Taron ya samu halartan wasu shugabannin jam’iyyar, da sauran jami’an jam’iyyar da kuma fitattun mambobi daga kananan hukumomi daban-daban zuwa babban birnin tarayya.

Da yake jawabi a taron, Sakataren APC na jihar Adamama, Dr. Raymond Chidama, ya ce yin rijistar ta yanar gizo zai kawo sauyi kan yadda jam’iyyar ke kula da bayanan membobinta da tsare-tsaren ta.

Shi ma da yake magana, Sakataren tsare-tsaren APC na jihar kuma Mai Gudanar da aikin yin rijistar ta yanar gizo, Mustapha Ribadu, ya ce shirin ya zama dole bayan an yi nazari sosai kan yadda jam’iyyar ta gudanar da zabenta idan aka kwatanta da ikirarin membobinta.

Ribadu ya ce sake tantancewa da inganta rajistar membobin zai taimaka wajen sake gina jam’iyyar bisa ga tushe na sahihanci da daidaito.

Wani fitaccen ɗan jam’iyyar kuma mai neman takarar gwamna, Abdulrahman Haske, wanda shi ma ya yi jawabi a lokacin taron, ya ce yin rijista ta intanet zai ƙara ƙarfafa APC a shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *