Jam’iyyar ADC ta kaddamar da shugabancin riko a Adamawa

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Adamawa ta kaddamar da kwamitin zartarwa na wucin gadi don jagorantar al’amuran jam’iyyar har sai an zabi sabbin shugabanni a hukumance.
Da yake jagorantar bikin rantsar da shi, Mataimakin Shugaban ADC na Yankin Arewa maso Gabas, David Lawal Babachir, ya ce masu ruwa da tsaki sun amince su kafa tawagar rikon kwarya don daidaita jam’iyyar da kuma shirya ta don babban zaben 2027.
Babachir, wanda ya yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) ya amince da sabon tsarin bayan tattaunawa da bin kundin tsarin jam’iyyar.
Ya jaddada cewa ba za a lamunci rashin da’a ko rashin biyayya a jam’iyyar ba.A cewarsa, Shugaban ADC na Kasa, Sanata David Mark, ya sake jaddada kudirin jam’iyyar na tabbatar da kundin tsarin mulkinta, yana mai gargadin cewa duk wanda ya saba wa ka’idojinta “ba shi da matsayi a ADC.
“A jawabinsa na karɓar muƙamin, sabon shugaban riƙon ƙwarya, Barista Sadiq Dasin, ya nuna godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar saboda amincewar da suka yi wa tawagarsa.
Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa ya yi alƙawarin haɗa kan jam’iyyar tare da ba da fifiko na musamman ga mata da matasa.
Ya ƙara da cewa zai tabbatar da cewa duk wani taron majalisar da za a yi nan gaba a jihar zai kasance mai gaskiya, adalci, da kuma sahihanci.
