Jami’an tsaro sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

0
1000050013
Spread the love

Jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kai hari da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Hakan na kunshe ne a cikin wani sako da wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya fitar a shafinsa na X ranar Litinin.

A cewar sa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Agusta da misalin karfe 9:45 na dare. a lokacin da aka samu labarin cewa ’yan bindiga dauke da makamai sun nufo, kauyen Unguwar Makera.

“Dakarun Operation FANSAN YANMA da suke aiki tare da ‘yan sanda da ’yan banga, sun yi gaggawar shiga yankin, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka yi watsi da manufarsu ta yin garkuwa da mazauna yankin tare da sace dabbobi,” inji Makama.

Makama ya ci gaba da cewa wasu mazauna garin Muhammad Inuwa da Babale Abdulkarim sun samu rauni a kafa yayin harin.

An kai su babban asibitin Malumfashi inda suke samun kulawa kuma suna cikin koshin lafiya.

Ya kara da cewa tun daga lokacin ne jami’an tsaro suka fadada sintiri zuwa yankin Garin Gafa da ke karamar hukumar Kafur domin zakulo wadanda ake zargi da gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *