Israel ta kai hari a birnin Doha

0
1000146343
Spread the love

Isra’ila ta ƙaddamar da hari kan babban birnin Qatar, Doha, da nufin kai hari kan manyan jagororin Hamas.

Rahotanni sun bayyana cewa jagororin sun je Doha ne domin tattaunawa kan kudurin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na baya bayan nan.

An ji ƙarar fashewa da dama a yankin Katara da ke birnin.

Wani babban jami’i a Isra’ila ya shaida wa manema labarai a ƙasar cewa waɗanda aka kai wa harin sun haɗa da Khalil al Hayya, shugaban Hamas a Gaza.

Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar yankin. Qatar ta yi Allah-wadai da harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *