Hukumar Kwastam ta kama Man Fetur na Naira Miliyan 181.6 a Adamawa

0
1000345476
Spread the love

Rundunar Operation Whirlwind ta Kwastam ta Najeriya ta kama wani jirgin ruwa mai dauke da man fetur wanda darajarsa ta kai naira Miliyan N181,603,515 a jihar Adamawa.

Kodinetan kasa na Operation Whirlwind, Mataimakin Kwanturolan Kwastam, ACG Kolapo Oladeji ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Yola ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa hukumar kwastam ta sami gagarumin ci gaba a cikin aikin da ake yi na kare mutuncin albarkatun kasar bisa ga muhimman dokokin hukumar kwastam ta Najeriya kamar yadda aka tsara a cikin dokar hukumar kwastam ta Najeriya, 2023.

ACG Oladeji ya ce jami’ansa, ta hanyar ayyukan leken asiri da aka gudanar cikin makonni takwas (8) cikin lokuta hamsin da biyar (55), sun kai wadannan hare-hare a wasu garuruwa da kauyuka a jihar Adamawa.

Ya bayyana cewa bisa ga wadannan umarni, rundunar Operation Whirlwind zone ‘D’ ta sake sanya dukkan kayan aikinta a fadin jahar domin tabbatar da cewa iyakar ta kasance cikin kula mai kyau.

Ya bayyana cewa wadannan ayyukan ya kawo cikas ga masu kawo cikas ga tattalin arzikin ƙasa su gudanar da ayyukansu na fasa kwauri.

Ya sanar da cewa, duk da gargadin da aka yi wa jama’a game da hare-haren da ba bisa ka’ida ba ga jami’an da ke gudanar da ayyukansu na doka, har yanzu ana ci gaba da samun karuwar hare-haren da ake kai wa jami’an.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *