Harin jirgi mara matuki ya janyo cikas wajen tashin jiragen sama a Dubai
Wani hari da jirgin yaki mara matuki ya kai a ranar Litinin ya haifar da gobara a wani tankin man fetur kusa da filin jirgin sama na Dubai, lamarin da ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na dan lokaci.
An karkatar da wasu jiragen sama saboda harin da dakatar da tashin jirage na wani lokaci kuma an sauya akalar wasu zuwa wasu filayen jiragen sama kamar Al Maktoum International Airport.
Daga baya kamfanonin jiragen sama sun fara dawo da wasu ayyukansu kadan-kadan bayan shawo kan gobarar.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da kawancen Amurka da Isra’ila ke ci gaba da tsananta.
Iran na ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage mara matuki zuwa kasashen yankin Gulf, ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Rahotanni sun nuna cewa fiye da makaman linzami da jirage marasa matuki 2,000 aka harba a yankin tun bayan fara yakin.
Lamarin ya shafi ababen more rayuwa kamar filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa da wuraren ajiyar mai.
