Harin ƙunar baƙin wake a massalaci ya yi ajalin mutum bakwai a Maiduguri

0
1000051878
Spread the love

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an ji ƙarar abin fashewa a wani masallaci a birnin Maiduguri na jihar Borno, wanda zuwa yanzu ya yi ajalin aƙalla mutum 7, sannan wasu da dama suka jikkata.

Kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai wannan harin, wanda ake kyautata zaton na ƙunar baƙin wake ne.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun fara da jin ƙara mai ƙarfin gaske, daga nan kuma sai baƙin hayaƙi ya turnuƙe masallacin da ke kasuwar Gamborou a jihar a lokacin sallar Magariba.

Malam Abuna Yusuf na cikin jagororin masallacin, ya shaida wa AFP cewa mutum takwas ne suka rasu.

Jihar Borno da kewaye na fama da hare-haren masu tada ƙayar baya na Boko Haram, inda suke kai hare-hare a makarantu da wuraren ibada da kasuwanni, duk da yake a ‘yan shekarun nan an samu kwanciyar hankali a jihar.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce mutum bakwai ne suka rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *