Gwamnatin Najeriya ta maka El-Rufai a kotu kan naɗar wayar Nuhu Ribadu

Gwamnatin Najeriya ta shigar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ƙara a gaban kutun taraya bisa zargin sa da naɗar wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ba tare da izini ba.
A ranar 13 ga watan Fabarairu ne lokacin da ya yi fira da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa Nuhu Ribadu ne ya bayar da umarnin a kama shi, kuma ya gano hakan ne bayan “wani” ya saurari tattaunawar waya ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu.
A cikin ƙarar da gwamnatin ta shigar, ta ce “Kai, Mallam Nasiru El-Rufai, ka amince a hirar da ka yi cewa kai da abokan aikinka kun naɗi wayar Nuhu Ribadu, ba bisa doka ba”.
Wannan ya saɓa da sashe na 12 (1) na Dokar hanawa da daƙile laifukan Intanet ta 2024.
A tuhuma ta biyu kuma gwamnatin tarayya na zargin Nasiru El-Rufai da cewa ya san wasu da suke naɗar wayar mutane ba bisa ƙa’ida ba amma bai kai ƙarar su ga hukumomin tsaro ba inda takardar ƙarar ta ce “wannan ya saɓa da sashe na 27 (b) na Dokar hanawa da daƙile laifukan Intanet, wanda hakan laifi ne.
A makon da ya gabata ne wasu jami’an tsaro suka yi yunƙurin kama El-Rufai a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, bayan komawa Najeriya daga Masar.
