Gwamnatin Najeriya ta ayyana hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

0
1000389753
Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga Disamba da kuma 1 ga Janairu 2026, a matsayin ranakun hutu na ƙasa.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan inda ya ce an ba da hutu a waɗannan ranaku ne domin murnar Kirsimeti da rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti wato Boxing day da kuma sabuwar shekara.

Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya “Da su yi tunani kan darajoji na soyayya da zaman lafiya da tawali’u da sadaukarwa da murnar haihuwar Yesu Almasihu.

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba, da su yi amfani da lokacin bukukuwa wajen addu’a don zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *