Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafi

0
1000473730
Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin tantancewa tare da ɗaukar bayanan ’yan kasuwar da gobarar kasuwar Singer ta shafa domin tsara yadda za a bi matakan ba su tallafi.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Asabar inda ta ƙone shaguna da tebura fiye da 1,500, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai yawa ga ’yan kasuwa.

Tuni gwamnatin tarayya ta bai wa waɗanda abin ya shafa tallafin Naira biliyan biyar, baya ga gudummawar da wasu hukumomi da daidaikun jama’a suka bayar.

Hukumomin jihar sun sanar da fara aikin tantance ’yan kasuwar ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha wato SEMA.

Hukumar ta bayyana cewa duk lokacin da aka samu iftila’i irin wannan, sukan je su ƙididdige tare da ɗaukar bayanan waɗanda abin ya shafa domin sanin yadda za a taimaka musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *