Gwamnatin Enugu ta kama likitan bogi, ta kuma rufe asibiti ba bisa ka’ida ba

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Enugu ta kama wani likitan bogi tare da rufe wani asibiti ba bisa ka’ida ba a Obollo-Etiti da ke karamar hukumar Udenu saboda yana aiki ba tare da lasisi ba kuma yana jefa rayukan marasa lafiya cikin haɗari.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar, Ugodu Avemaria, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, Kwamishinan Lafiya, Farfesa George Ugwu, ne ya shirya aikin, wanda ya gano shaidu masu ban mamaki na rashin tsafta da rashin lafiya na cibiyar.
Sanarwar ta ambaci likitan bogi a matsayin Mista Kenneth Mamah da kuma asibitinsa, mai suna St. Joseph Memorial Hospital, Ada-ulo Obollo-Etiti Community.
