Gwamnan Sokoto ya buƙaci masu hali su riƙa ciyar da masu azumi

0
1000373459
Spread the love

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya yi kira ga masu hannau da shuni a jihar su taimaka wajen cikyar da mabuƙa a faɗin jihar.

Gwamnan ya yi kirane ne a lokacin da ya kai ziyara wata cibiyar da gwamnatinsa ke ciyar da masu azumi.

Ya ce gwamnatinsa na bayar da tallafin abincin buɗe-baki ga masu azumi a jihar, wanda ya ce za a riƙa bai wa aƙalla masu azumi 34,000 a kullum.

A lokacin ziyarar, gwamnan ya ziyarci cibiyoyin da ke titin Clapperton da Lodge Road da Gidan Dallatu da asibitin ƙwararru da yankin Madunka, inda ya yaba da ingancin abincin da ake rabawa ga mutane.

Gwamnan ya ƙara da cewa an samu ci gaba a irin ingancin abincin a bana, idan aka kwatanta da irin abincin da aka raba a shekarar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *