Gwamnan Kano ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai wa shugaba Bola Tinubu ziyara a fadarsa da ke Abuja.
Gwamnan ya isa fadar shugaban ƙasar ne a yammacin yau Litinin.
Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke ƙara tabbata na sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Siyasar Kano ta shiga ruɗani a baya bayan-nan bayan rahotannin sauya sheƙar gwamna Yusuf, wani abu da jagororin NNPP da kuma uban jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka nuna adawa a kai.
Lamarin ya janyo saɓani a cikin jam’iyyar, musamman tsakanin magoya bayan gwamnan da kuma waɗanda ke mubaya’a ga tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Kwankwaso ya assasa.
