Gwamna Fintiri Ya Amince Da Biliyan 8 domin biyan bashin Fansho/Gratuti

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya amince da Naira Biliyan 8 domin biyan bashin fansho a jihar Adamawa.
Babban Sakataren Hukumar Fansho na Jihar, Mohammed Usman, ya bayyana cewa Naira biliyan 5 za a baiwa ‘yan fansho na Jihohi da Biliyan 3 ga ‘yan fansho na kananan hukumomi.
Ya kara da cewa basussukan ya samo asali ne daga gazawar gwamnatin da ta shude ba ta biya ba a tsawon shekaru hudu da ta yi tana mulki.
Ya tabbatar da kudirin gwamnatin Fintiri na kawar da duk wasu basussukan fansho da ake bin su.
