Gwamna Ahmadu Fintiri ya karawa matasan NYSC kudin Alawus daga N20,000 zuwa N30,000.

0
1754056011830
Spread the love

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da sake duba kudaden alawus da ake biyan masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke aiki a jihar Adamawa daga N20,000 zuwa N30,000 duk wata.

An bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin bikin rantsar da sashe na Batch B Stream I Orientation Course na shekarar 2025 da aka gudanar a sansanin NYSC Permanent Orientation Camp da ke Damare a karamar hukumar Girei.

Sanye da kayan bautar kasa na NYSC, Gwamna Fintiri ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaban matasa da kuma kyautata jin dadin ‘yan NYSC da aka saka a jihar.

Ya kara da cewa wannan karin ya nuna kokarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da yanayi mai kyau na hidima, da suka hada da tallafawa a kai a kai da kayan abinci da sauran ayyukan jin dadi.

“A matsayinmu na gwamnati, mun himmatu wajen inganta jin dadin ‘yan NYSC, wannan karin ya dace da alkawarin da muka yi na samar muku da yanayi na sada zumunci da goyon baya,” in ji Gwamnan.

Gwamna Umaru Fintiri ya kuma bayyana cewa shirye-shirye sun kai wani mataki na gina sabon sansanin NYSC a jihar.

Ya umurci Kodinetan NYSC na Jiha da ta sa matasan na NYSC cikin koyon sana’a da suka dace a fannin gine-gine, injiniya, a dai sauran su.

Da yake taya sabbin ’yan NYSC da aka rantsar bisa nasarar kammala tafiye-tafiyen da suka yi na karatu, Gwamnan ya yi musu maraba da zuwa Jihar Adamawa tare da ba su tabbacin goyon bayan gwamnati.

Ya bayyana su a matsayin abokan huldar dabarun aiwatar da muhimman manufofin gwamnati, musamman a bangaren ilimi.

A nasa jawabin kwamishinan matasa kuma shugaban hukumar NYSC ta jihar Barista Wali Yakubu ya bukaci ‘yan matasan NYSC da su dauki kwas din koyar da sana’o’in hannu da muhimmanci, su yi biyayya ga dokokin sansani, da kuma rungumar damar koyon sana’o’i da za su inganta dogaro da kai fiye da shekarar hidimarsu.

Ko’odinetan NYSC na jihar, Misis Osoro Caroline, ta bayyana farin cikin ta da da’a da sabbin ‘yan matasan NYSC suka nuna tun lokacin da suka isa sansanin.

Ta ce an shirya kwas din wayar da kan jama’a ne domin samar musu da kayan aikin da ake bukata domin bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa.

Ta yabawa Gwamna Fintiri kan karin albashi, da tsare-tsaren sa na sansanin NYSC, da sauran tsare-tsare na walwala ga ‘yan NYSC, inda ta bayyana shi a matsayin jagora mai hangen nesa kuma shi ne tushen karfafa matasa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *