Guardiola na fatan Haaland zai murmure kafin wasansu da Burnley

0
1000179129
Spread the love

Pep Guardiola na fatan Erling Haaland zai murmure kafin ranar Asabar da za su fuskanci Burnley a gasar Premier League.

An sauya ɗan ƙwallon Norway a wasan da aka tashi 1-1 tsakanin Arsenal da Manchester City ranar Lahadi a Etihad, inda Guardiola ya ce ɗan wasan na fama da ciwon baya.

City tana ta tara a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki takwas tsakani da Liverpool mai rike da kofin bara.

City tana fama da ƴan wasan dake jinya da suka haɗa da Rayan Cherki da Rayan Ait-Nouri da Omar Marmoush, yayin da aka sauya Abdukodir Khusanov a wasa da Arsenal a karshen mako.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *