Gomnatin tarayya ta tabbatar da Jajircewarta ga ‘Yancin addini, inda tayi watsi da rahoton Amurka kan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton Amurka kan ‘yancin Addini a Najeriya, inda ta sake fasalta kalubalen tsaron Ƙasar a matsayin wani bangare na fannin yaki da ta’addanci a yankin.
A cikin wata sanarwa, Kimiebi Ebienfa, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, ta bayyana cewa wannan rashin zaman lafiya yana faruwa ne sakamakon wasu bukatu na musamman a Yammacin Afirka da Sahel.
Gwamnati ta sake jaddada kudirinta na kare dukkan ‘yan kasa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.Sanarwar ta yaba da kokarin Sojojin Kasa kuma ta nuna goyon baya ga wadanda tashin hankali ya shafa.
Kimiebi Ebienfa ta jaddada matsayin Najeriya a matsayin kasa mai mutunta yancin addini da wacce ke daraja hakkin juna ba kamar yadda Amurka ke ikirari ba.
Duk da rashin jituwa kan kimanta rahoton, sanarwar ta tabbatar da kawancen Najeriya da Amurka kuma ta bayyana sha’awar ci gaba da hadin gwiwa wajen neman zaman lafiya, ‘yanci, da dimokuradiyya.
