Gawuna, ya fice daga APC zuwa ADC

0
Dr Nasir Gawuna

Dr Nasir Gawuna tsohon dan takaran gwamnan Kano a Jam'iyyar APC

Spread the love

Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2023 karkashin jam’iyyar APC, Yusuf Gawuna, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC.

Rahotanni sun nuna cewa matakin na Gawuna na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, inda ‘yan siyasa ke sauya sheka daga Jam’iyyun su.

Komawar tasa zuwa ADC na iya haifar da sauyi a tsarin siyasar Kano, ganin irin tasirin da yake da shi a jihar.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani daga gare shi kan dalilan da suka sa ya fice daga APC, amma ana sa ran zai bayyana matsayinsa nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *