Ganduje ya musanta shirin ficewa daga APC zuwa zuwa ADC

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya yi watsi da rahotannin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Ganduje ya bayyana rahotannin shiga jam’iyyar ADC a matsayin labaran karya.A ranar 27 ga watan Yuni, Ganduje ya ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa, saboda matsalar lafiya.
Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, a wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa.
Watanni biyu bayan murabus dinsa na shugaban jam’iyyar APC na kasa, wasu rahotanni na cewa Ganduje da mabiyansa na shirin ficewa daga APC zuwa ADC.
Sai dai mai magana da yawun Ganduje, Edwin Olofu, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Kano ya ci gaba da biyayya ga shugaba Bola Tinubu.
