Fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka karɓi katin zaɓe gabanin zaɓen Abuja- INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta bayyana cewa fiye da masu zaɓe miliyan 1.5 ne suka karɓi katin zaɓe a duk faɗin babban birnin tarayya, Abuja kafin zaɓen majalisar kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Alhamis ta nuna cewa har zuwa ƙarshen karɓar katunan a ranar 10 ga Fabrairu, an yi rajistar masu zaɓe 1,680,315 a Abuja, inda mutum 1,587,025 suka karɓi katin zaɓe, yayin da katunan 93,290 suka rage ba a karɓa ba.
Hukumar ta jaddada cewa waɗanda suka yi rajistar zaɓe kuma suka ansa kati ne kawai za su samu damar kada kuri’a a ranar zaɓe.
INEC ta ce ta shirya dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaɓe mai gaskiya.
