Firaministan Japan Ishiba ya yanke shawarar yin murabus

0
1000121766
Spread the love

Firaministan ƙasar Japan Shigeru Ishiba ya yanke shawarar yin murabus a yau lahadi, inda ‘yan jam’iyyarsa suka yi kira da a kawo sauyi a harkokin shugabanci biyo bayan rashin kyakkyawan sakamakon da aka samu a zaben ‘yan majalisar dattawan ƙasar da aka gudanar a wannan bazarar.

Daukar matakin na murabis na zuwa ne kasa da shekara guda bayan da shugaban mai shekaru 68 ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP) mai rinjaye a tarihi, inda ya zama shugaban gwamnati.

Tun daga wannan lokacin, jam’iyyar LDP ta yi fama da kaye sau biyu a zabukan da aka gudanar a majalisun biyu.

Kafar yada labarai ta NHK ta ruwaito cewa Ishiba na son kaucewa rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyarsa, yayin da jaridar Asahi Shimbun ta ce ba zai iya ci gaba da yin tir da kiraye-kirayen da ake yi na yin murabus daga mukaminsa ba.

A yammacin jiya asabar ne Ishiba ya gana da ministan noma Shinjiro Koizumi da tsohon firaministan ƙasar Yoshihide Suga, wani babban jigon jam’iyyar, wadanda suka bukaci ya yi murabus, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

A kwanakin baya ne dai wasu manyan jami’an jam’iyyar LDP guda hudu ciki har da sakatare-janar Hiroshi Moriyama suka yi tayin yin murabus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *