Firaministan Faransa zai yi Murabus

Firaiministan Faransa, Francois Bayrou na dab da yin murabus bayan rasa yin rinjaye a kuri’ar yankan kaunar da aka kada a majalisar dokokin kasar a jiya Litinin.
Yana dai son ya rage kudaden da ake kashe wa al’ummar kasar ne domin magance bashin da kasar ke fama da shi, to amma ya rasa samun cikakken goyon baya akan hakan.
Murabus din nasa zai jefa kasar cikin rikicin siyasa inda a yanzu doke shugaba Emmanuel Macron ya nada sabon firaiministansa karo na bakwai tun bayan da hau mulki a shekarar 2017.
