Fintiri ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 583 ga Majalisar Dokokin Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya gabatar da kasafin kuɗi na sama da Naira biliyan 583 na shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar inda ya karanta jimillar Naira biliyan 583,331,380,496, wanda kashi 64.07 cikin ɗari na kashe kuɗi ne na manyan ayyuka, wanda ya kai Naira biliyan 373,690,964,682; da kuma kashi 35.93 cikin ɗari na kashe kuɗi na yau da kullun, wanda ya kai Naira biliyan 209,640,964,682.

Gwamnan ya nuna cewa babban kaso na kasafin kuɗi, sama da Naira biliyan 120, ya kasance na Ma’aikatar Ayyuka da Ci Gaban Makamashi ta Jihar don ci gaba da aikin gwamnati da sauran ayyukan da ke kewaye da babban birnin Yola, da sauran sassan jihar.
A cewar gwamnan, ilimi zai kasance mafi girman kaso na gaba a kasafin kudin, inda zai biyo bayan ma’aikatar da wani kaso na kasafin kudin da ya kai Naira biliyan 40, yayin da za a ware Naira biliyan 31.9 na samar da lafiya.

Gwamnan ya gode wa Majalisar Dokoki saboda hadin gwiwar da ya samu daga ‘yan majalisa daga dukkan jam’iyyu, sannan ya yi kira da a gaggauta amincewa da kudirin kasafin kudin 2026.
Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar, Bathiya Wesley, ya yi wa bangaren zartarwa na jahar jawabi kan yadda ta aiwatar da kasafin kudin shekarar da ke tafe.
Shugaban Majalisar ya ce Majalisar za ta fara aiki nan take domin tabbatar da cewa an yi wa kudirin kasafin kudin 2026 bita da sauri kuma an zartar da shi yadda ya kamata.
